1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

A karon farko cikin tarihin Jamus AfD ta samu nasara

September 1, 2024

Jam'iyyar AfD da ke kyamar baki ta zo a matsayin farko na zaben da ya gudana a jihar Thuringia da ke gabashin Jamus, sannan tana biya wa jam'iyyar CDU da ke da ra'ayin mazan jiya baya a jihar Saxony.

Guda daga cikin 'yan takarar zaben majalisa a Thuringia, Bodo Ramelow, a yayin kada kuri'a
Guda daga cikin 'yan takarar zaben majalisa a Thuringia, Bodo Ramelow, a yayin kada kuri'aHoto: Ronny Hartmann/AFP/Getty Images

Alkaluma sun nunar da cewa jam'iyyar Alternative for Deutschland AfD) ta samu 30.5 zuwa 33.5% na kuri'un da aka kada yayin da  CDU ta samu kashi 24.5% na kuri'un da aka kada a Thuringia. Sai dai a jihar Saxony, CDU ce ke kan gaba da 31.5 zuwa 32% yayin da AfD da ke kashi 30 zuwa 31.5% na kuri'un da aka kada.

Karin bayani: Jamus: An kawo karshen rikicin siyasar Thuringia

Wadannan tagwayen zabukan sun gudana ne mako guda bayan kashe mutane uku da  wani dan Syria ya yi a garin Solingen, wanda ya girgiza kasar tare da sake farfado da muhawara kan shige da fice a Jamus.

Karin bayani:Zaben jihar ya dauki hankali a Jamus 

Amma dai nasarar da AfD ta samu a Thuringia na zama na farko a kasar Jamus tun bayan yakin duniya na biyu, ko da yake manufofinta na wariya sun sa sauran jam'iyyun Jamus nesanta kansu da hada gwiwa da ita don kafa gwamnati a jihar.