1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

A karon farko Italiya ta biya diyya kan barnar 'yan Nazi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 4, 2024

Sojojin Jamus ne suka kashe Metello Ricciarini tare da wasu mutane 243 a yankin Civitell, mai nisan kilomita 220 daga birnin Rome, a ranar 29 ga watan Yunin shekarar 1944.

Hoto: Michele Nucci/LaPresse/ZUMA/picture alliance

A karon farko kasar Italiya ta biya diyya kan barnar da 'yan Nazi suka aikata ta kisan kare dangi ga yahudawa, inda ta biya Euro dubu dari takwas ga iyalan wani mutum da aka kashe a shekarar 1944, kamar yadda lauyan iyalansa Roberto Alboni ya tabbatar a Larabar nan.

Karin bayani:Steinmeier ya nemi afuwa kan laifukan Nazi

Biyan diyyar na zuwa bayan shafe tarin shekaru ana shari'a a kai, inda aka yi amfani da asusun gwamantin kasar wajen biya, lamarin da ka iya sa wasu iyalai su garzaya kotu don neman ta su diyyar kisan da aka yi wa magabatansu, a yayin yakin duniya na biyu.

Sojojin Jamus ne suka kashe Metello Ricciarini tare da wasu mutane 243 a yankin Civitell, mai nisan kilomita 220 daga birnin Rome, a ranar 29 ga watan Yunin shekarar 1944.

Karin bayani:An sace wasu kayan tarihi na Holocaust a Jamus

Ko a shekarar 1962 sai da gwamnatin Jamus ta biya Italiya diyyar Deutschmark miliyan 40, kwatankwacin sama da Euro biliyan daya a yanzu, kan barnar da 'yan Nazi suka aikata.