SiyasaMexiko
Karon farko mace na shirin lashe zaben shugaban kasar Mexico
June 3, 2024Talla
Claudia Sheinbaum ta kama hanyar zama mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar kasar Mexico, bayan samun kashi 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben da aka gudanar ranar Lahadi.
Karin bayani:Mexico: Zaben mace shugabar kasa ta farko
Wadda ke biye mata a matsayi na biyu da kashi 29 cikin 100 na kuri'un ita ma mace, mai suna Xochitl Galves, fitacciyar 'yar kasuwa kuma 'yar majalisar dattijai yanzu haka.
Karin bayani:Hadarin mota ya hallaka bakin haure 'yan Afirka a Mexico
Wanda ke a mataki na uku ne dai namiji mai suna Jorge Alvarez Maynez, mai kashi 11 cikin 100 na kuri'n zaben.