1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Jam'iyyar PDP ta zabi sabbin shugabanninta

Ubale Musa | AH Hassane
November 14, 2025

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta kammala babban taronta na kasa, inda ta zabi sabbin shugabanni tare da korar wasu kusoshinta da ta zarga da makarkashiyar durkusar da ita.

Tutar PDP
Tutar PDPHoto: DW/K. Gänsler

Duk da kasancewa mafi  dadewa a cikin fagen siyasar tarayyar Najeriya, 'yan sao'i da ke tafe dai na da tasirin gaske bisa makomar jam'iyyar PDP ta adawa.

Wata sanarwar PDP  dai ta sa kafa ta shure barazana ta kotuna, da ma adawar wani bangare cikin gidan jam'iyyar, tare da yanke hukuncin fara babban taron.

To sai dai kuma rabuwar na kara bayyana in da rasan PDP a mafi yawa na kudanci na kasar ke shirin su kauracewa taron.

Tsohon hoto na taron siyasaHoto: Olukayode Jaiyeola/picture-alliance/dpa

Can ma a arewa dai PDP na kallon tawaye daga  jihohi irin na su Sokoto da Jigawa da ya'yansu ke fadin ba su shirin taka rawa cikin babban taron da za'a fara a garin Ibadan.

Hira da Aminu Waziri Tambuwal

03:00

This browser does not support the video element.

Tun farko wata kotu a Abuja ta amince da bukatar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido na dakatar da babban taron duk da kasancewar mafi yawa na ya'yan jam'iyyar sun isa birnin  na Ibadan.

Ruhi da kila ma makomar  PDP bayan taron Ibadan din da,i daga dukka na alamu na shirin ta'allaka bisa arewacin kasar da ke da gwamnonin jam'iyyar har guda Bakwai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani