1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila ta yi barin wuta a Gaza sa'o'i bayan sulhu da Hamas

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
January 16, 2025

Sojojin Isra'ila sun yi luguden wuta a yankin Gaza sa'o'i bayan da kasar ta cimma yarjejeniyar tsagaita buda wuta da kungiyar Hamas

Gazastreifen | Zerstörung nach israelischem Luftangriff in Tuffah
Hoto: Omar AL-QATTAA/AFP

Ma'aikatar tsaron Falasdinu ta ce dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta a wasu sassan Gaza tare da kashe fararan hula 7 a yayin da wasu gommai suka jikkata, kwana daya bayan sanar da kulla yarjejeniyar tsagaita buda wuta a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.

Karin bayani : Isra'ila da Hamas sun cimma tsagaita wuta a Gaza

A cikin wata sanarwar da suka fitar, hukumomin yankin Falasdinu sun ce an kai harin ne a wata unguwa mai suna Rimla da ke tsakiyar Gaza. Ko a wannan Laraba, sai da hukumomin yankin Gaza suka tabbatar da mutuwar fararen hula 20 a wani barin wutar da dakarun Isra'ila suka yi wa yankin, sa'o'i a gabanin sanar da cimma yarjejeniyar sulhu.