1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iAfirka

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 13 a Kenya

Suleiman Babayo AH
April 25, 2024

A birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar Kenya ambaliyar ruwa ta halaka mutane 13 yayin da gwamnatin kasar take ci gaba da neman hanyoyin matsalolin da suka biyo bayan ambaliyar duk da suka daga 'yan adawa.

Kenya | Ambaliyar ruwa a birnin Nairobi
Ambaliyar ruwa a birnin Nairobi na kasar KenyaHoto: Gerald Anderson/Anadolu/picture alliance

Ruwan sama da ake ci gaba da shekawa ya haifar da ambaliyar da ya halaka fiye da mutane 10 a birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar Kenya. Hukumomi tsaro sun tabbatar da gano mutanen da suka halaka sakamakon ambaliyar.

Tuni Shugaba William Ruto na kasar ta Kenya ya kira taron gaggawa a wannan Alhamis, domin duba hanyoyin magance matsalolin da suka taso sakamakon ambaliyar ruwan, sai dai masu sukar gwamnati suna zargin shugaban da jan kafa wajen daukan matakan da suka dace. Gwamnati ta Kenya ta tura jami'an tsaro domin tabbatar da taimakon mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa.