1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Masar an rusa hukumar rubuta tsarin mulki

Usman ShehuApril 10, 2012

Kotu a ƙasar Masar ta soke hukumar rubuta sabon kuddin tsarin mulkin ƙasar da ake taƙaddama a kansa

Sabbin 'yan majalisar dokokin Masar, cikin zauren majalisar.
Ägypten ParlamentHoto: picture-alliance/dpa

Kotun a ƙasar Masar ta soke hukumar rubuta tsarin mulki. Lawyoyi masu shigar da ƙara sun soki matakin da yan majalisa suka ɗauka, inda suka ware kashi 50 cikin ɗari na kujerun majalisar dokokin ƙasar, ga mutanen da za su kasance wakilai a wannan hukumar da za ta rubuta sabon kundin tsarin mulki. Ana saran a yammacin yau za a turawa majalisar dokoki wannan hukuncin da kutun ta yanke. Dama dai jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi, da ɓangaren kiristocin ƙasar ta Masar duk sun janye wakilansu daga wannan hukumar da ake taƙaddama a kanta, inda suke zargin masu kaifin Islama sun mamaye ta. Kundin tsarin muli na wucin gadi da ake amfani da shi yanzu haka a ƙasar Masar ya tanadi kafa wata hukama da za ta rubuta sabon kundin tsarin mulki, to amma bai fayyace ko yan majalisar dokoki na iya kasancewa wakilai a hukumar ko a'a. Sabon kundin tsarin mulkin da za a rubuta dai shine zai shata ƙarfin da shugaban ƙasa zai iya samu a ƙasar da take farfaɗowar daga mulkin kama karya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mouhamadou Awal