1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A naɗa sabuwar shugabar asusun IMF

June 28, 2011

Ministan tattalin arziki ta ƙasar Faransa Christine Lagarde ta kasance mata ta farko da aka zaɓa akan masayin

Christine Lagarde sabuwar shugar asusun bada lamuni ta IMFHoto: AP

Kwamitin Zartaswa na asusun bada lamuni na duniya ya zabi Christine Lagarde ministan tattalin arziki ta ƙasar Faransa a masayin sabuwar shugabar Asusu IMF.

Lagarde yar shekaru 55 da haifuwa ta kasance macce ta farko da zata riƙe muƙamin bayan da tsofon shugaban hukumar Dominique Strauss Khan wanda ke fuskantar tuhuma a gaban shara'a kan laifin yin fayɗe ga wata matar mai yin shara a Hotel a Amurka ya yi marabus.

Tun can da farko dai masu aiko da rahotannin sun ce zaɓin na Christine ba zai samu wata jayaya ba bayan da ta samu goyon bayan Amurka a gaban ɗan takarar ƙasar Mexiko.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad tijani Lawal