1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yajin aikin jami'o'i a Najeriya

Muhammad Bello SB
October 28, 2024

Manya da kananan ma'aikatan jami'o'in Najeriya sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani, bisa wasu bukatunsu da suka ce gwamnati ta yi kememen biya musu, duk kuwa da zaman yarjejeniyoyi da ake ta faman yi.

Daliban Najeriya na zanga-zamga
Daliban Najeriya na zanga-zamgaHoto: AP/picture-alliance

Ma'aikatan dai jami'o'in manya da kanana sun ce yajin aikin da suka fara duk kuwa da jan kunne ga hukumomin kasar. Babban dai batun da suke kokawa kai shi ne na kin biyan albashin watanni hudu da suke bi tun shekara ta 2022. Wannan yajin aikin dai, bisa ga duk alamu, duk da ba na malaman jami'o'i ba ne, zai durkusar da harkokin makarantun.

Karin Bayani: Najeriya: Kungiyar malamai ASUU ta janye yajin aiki

Daliban NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP via Getty Images

Sai dai kuma yayin da manya da kananan ma'aikatan jami'o'in ke fara yajin aikin, kungiyar Malaman jami'o'in ita kanta ta ja kunnen gwamnatin tarayya kan wasa da hankali tsawon lokaci, tare da korarin ita ma za ta fara haramar tsunduma kan yajin aikin, kan bukatu da koke-koke da shugaban kungiyar ta Malaman na jami'o'i ta ASUU ya tabbatar. Yanzu dai bayanai sun tabbatar da cewar wannan yajin aiki na sai baba ta gani da dalibai da iyaye ke tir da shi, ya fara kankama a da daman jami'o'in kasar.

 

A shekara ta 2022 dai, sai da ASUU ta dau tsawon watanni 8 tana yajin aiki, ba kuma tare da gwamnatin Najeriya, karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta rusuna musu ba, illa dai kawai karatun dalibai ya tsaya, sannan an bar daliban da cabewar karatu koma dai karin zango na karatun.