1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga sun fatattaki kauyuka a Najeriya

May 14, 2024

Kimanin garuruwa 50 'yan bindiga suka kori al'ummar garuruwan a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara a yankin arewa maso yammacin Najeriya. Daga cikin Al'ummar garuruwan akwai sama da 500 da ke hannun 'yan bindiga.

'Yan bindiga sun fatattaki kauyuka a jihar Zamfara da ke Najeriya
'Yan bindiga sun fatattaki kauyuka a jihar Zamfara da ke NajeriyaHoto: Str/Getty Images/AFP

Hare-haren Yan bindigar dai ya yi kamari a wannan yankin na Zurmi abunda yasa Al'ummar yankin shiga tsaka mai wuya wannan mazaunin yankin ya ce kashe mutane da garkuwa da su ya zama ruwan dare a yankin abin da ya sa kullun suke cikin zullumi. Hon. Bello Hassan Shinkafi shi ne dan majalisar tarayya da ke wakiltar yankin ya tabbatar da yanda mutanensa ke cikin ukubar 'yan bindiga:

Karin Bayani: 'Yan bindiga sun sace mutane 150 a Zamfara

"Karamar hukumar Zurmi ba ta cikin zaman lafiya saboda kauyukansu kusan za su iya kai wa 50 da wani abu babu garin da mutane ke zaune garin saboda tashin hankali. Kuma duk sanda akazo sai kaji an dauki wani ko kuma an kashe wasu. Shekaran jiya sun kashe mutane uku sun kuma yi garkuwa da mutane 30 sannan an jikkata wasu da dama. Yanzu an yi garkuwa da mutane 500 koma idan ba su fi haka ba"

'Yan bindiga sun fatattaki kauyuka a jihar Zamfara da ke NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP

A karamar hukumar Birnin Magaji ma da ke jihar ta Zamfara ana can ana jimamin sace wasu mutane sama da 100 lokacin da ya bindiga suka kai samame lokacin ana tsaka da cin kasuwa. Sai dai a bangaren gwamnatin jihar ta Zamfara ta ce tana iyaka kokarinta na ci gaba da lalubo hanyoyin magance matsalar.

Gwamnatoci dai a duk matakai da ma jami'an tsaro na shan alwashin shawo kan kashe-kashen mutanen da garkuwa da su a jahohin arewa maso yanmacin Nigeria amma dai masana tsaro na ganin maganganun kamar sun zama roman baka saboda kullun hare-haren na kara ta'azzara.