A Pakistan bam ya kashe mutane da yawa
November 5, 2010Talla
Wani bam da ya tashi a ƙasar Pakistan ya hallaka mutane aƙalla 66. Bam ɗin wanda ya tashi cikin mallaci a dai-dai lokacin da ake sallar Juma'a, ya ragargaza masallacin, abinda ya sa matune dayawa suka maƙale ƙarƙashin gurabuzai. Wannan harin da ya faru a arewa maso gabacin ƙasar, shine mafi laƙume rayuka tun watanni biyu. Mahukunta sukace mutane dayawa suka jikkata, kuma da alamu yawan waɗanda suka mutu zai ƙaru. Wani mai aiko da labarai da yaga masallaci, yace tsaban girman bam ɗin, ɗaukacin masallacin ya rushe. A wannan yankin ne dai ƙasar Amirka ke yaƙi da yan ƙungiyar Alƙa'ida.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas.