A Saliyo cutar Ebola ta shiga fadar gwamnati
March 1, 2015Talla
Wannan labarin da ya fito daga ofishin Samuel Sam-Sumana maitamakin shugaban kasar ta Saliyo, ya mai da hannun agogo baya bisa murnar da aka yi a yaki da cutar, inda ta kai ga har gwamnati ta sake bude makarantun kasar, bisa fatan an shawo kan cutar ta Ebola. To amma a halinda ake ciki, gwamnati ta maido da daukar tsauraren matakai na hana zirga-zirga, bayan samun tabbacin kwayar cutar Ebola na buzuwa. An dai fi mayar da hankali ne kan masu kai-kawo da jiragen kwale-kwale a gabar tekun kasar. Kawo yanzu dai sama da mutane 9,500 suka mutu sakamakon cutar ta Ebola, tun bayan bullarta a kasar Gini shekara daya da watanni.