A Thailand an koma gidan jiya
July 30, 2010Talla
Rahotanin daga ƙasar Thailand sun ce da alama an koma ga samun ɓarkewar tashe tashen hankula a birnin Bankok, bayan da wani bam din yaa fashe a tsakiyar garin wanda ya hadasa mumunar rauni ga wani mutuman
Hukumar 'yan sanda ta ƙasar ta shaida cewa bam din, a naɗe shi ne a cikin wata jaka kuma aka ajiyeta a kusa da wata shara a wata unguwar da ke kusa da gine gine gwamnatin a daidai lokacin da ake samun yawan kai da kawo na jama'a
Tun a cikin watan Afrilu ne dai gwamnatin ƙasar ta kafa dokar ta baci, a duk faɗin ƙasar a sakamakon zanga zangar 'yan adawar ta nuna ƙin jinin gwamnatin da aka ƙwashe makonni ana yi, wace a cikinta mutane 90 suka mutu yayin da wasu 2000 suka jikata
Mawallafi: Abdurrahmane Hassane
Edita: Umaru Aliyu