Zaben gama gari a kasar Angola
August 23, 2017Talla
Bayan shekaru 38 a kan karagar mulki, a wannan Laraba zamanin mulkin shugaban kasa kuma shugaban gwamnatin Angola Jose Eduardo dos Santos yake kawo karshe, inda al'ummar kasar su kimanin miliyan tara da aka yi wa rajistar zabe suke kada kuri'arsu a kasar da ke yankin Kudu maso Yammacin nahiyar Afirka.
Ana dai tsammanin cewa jam'iyyar MPLA ta Shugaba Dos Santos za ta sake lashe mafi yawa na kujerun majalisar dokoki 220, wanda haka kuma zai ba ta damar ci gaba da rike mukamin shugabancin kasar.
Babban dan takararta dai shi ne ministan tsaron kasa Joao Lourenco.