A yau mahajjatan bana ke tsaiwar Arfa
October 14, 2013Talla
A wannan Litinin din ce mahajjatan bana ke yin tsayuwar Arfa a Mina wanda ke zaman koluwa na akin hajji kamar yadda addinin Islam ya bayyana.
Kimanin mahajjata miliyan biyu ne za su shafe yinin yau a filin na Arfat inda za su yi ta gudanar da aiyyukan ibada da suka hada da zikiri da addu'o'i da salloli har zuwa sanda rana za ta fadi.
Su ma dai sauaran al'umma da basu samu zuwa aikin hajjin na bana ba a sassan duniya musamman ma dai wanda suke da dama, sun bi sawun takwarorinsu da ke Saudi wajen yin azumi na nafila na ranar Arfa da sauran aiyyuka na Ibada, tare kuma da cigaba da yin shirin bukukuwan sallar layya da za a yi gobe Talata idan Allah ya kaimu.
Mawalalfi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu