A yau ne Bosco Ntaganda zai gurfana gaban kotu ICC
March 26, 2013Ana dai zargin Mr. Ntaganda ne da aikata laifukan da su ka danganci kisan kai da fyade da kuma tursasawa yara kanana shiga aiki soji a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo.
Yayin zaman kotun za a fara ne tabbatar da mutumin a matsayinsa na Bosco Ntaganda, daga bisani kuma a karanto masa laifukan da ake zarginsa da aikatawa kana a tantance harshe da zai fi fahimta yayin shari'ar sannan a karshe a dage zaman kotun zuwa wani lokaci da a za a fara sauraron karar.
A makon jiya ne dai Bosco Ntaganda a wani mataki da ba a taba ganin irin sa ba ya mika kansa ga ofishin jakadancin Amurka da ke Kigali inda ya bukaci da a mika shi ga kotun da ke hukunta laifukan na yaki da ke birnin Hague na kasar Holland domin yi masa shari'a.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadisou Madobi