1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mabiya addinin Kirista na gudanar bikin Kirsimeti

Ahmed Salisu
December 25, 2024

A yau Laraba ce mabiya addinin Kirista ke bikin Kirsimeti da aka saba yi a duk ranar 25 ga watan Disamba domin murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Kiristi, ranar da ke da matukar muhimmaci ga mabiya addinin na Kirisita.

BdTD I Indien, Christen feiern Weihnachten in Mumbai
Hoto: Punit Paranjpe/AFP

Tun daga jiya Talata da maraice ne dai aka fara shagulgula na bikin inda Paparoma Francis da ke jagorantar mabiya darikar Katolika ya jagoranci mabiyansa wajen yin ibada a majami'ar nan ta St. Peters Basilica da ke Vatican.

Nan gaba a yau ne kuma Paparoman zai yi jawabinsa na al'ada da ya saba yi a irin wannan rana ga mabiya addinin na Kirista, inda ake sa ran jawabin zai mayar da hankali kan rikicin da ake yi a yankin gabas ta tsakiya da kuma yakin da Rasha ke yi a kasar Ukraine.