A yau wa´adin Yan majalisar Pakistan ke karewa
November 15, 2007Talla
Shugaba Pavez Musharraf, na tattaunawa da jami´an gwamnatinsa, don cimma ƙudiri guda game da zaɓen gama gari, da ake ƙoƙarin gudanarwa.Ana sa ran taron zai naɗa Gwamnatin riƙon ƙwaryane da za ta ɗauki nauyin gudanar da zaɓen.A yau Alhamisne wa´adin ´Yan Majalisun dokokin ke ƙarewa.A waje ɗaya kuma tsoffin Faraministocin ƙasar biyu, wato Benazir Bhutto da Nawaz Sharif, na ci gaba da tattaunawar sulhu ta zama tsintsiya ɗaya maɗaurinki guda.Ɗaukar wannan mataki dai yazo ne, a ƙokarin haɗa hannu da hannaye guri guda ne, don ƙalubalantar matakin dokar ta ɓaci da Mr Musharraf ya kafa ne.Mr Musharraf dai ya ce dokar ta ɓacin, za ta taimakane wajen gudanar da zaɓe mai tsafta a ƙasar ne.