1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tebboune ya lashe zabe a wa'adi na biyu a Aljeriya

September 8, 2024

Taboune mai shekara 78 ya zama shafaffe da mai, abinda ya bashi damar samun nasara a kan abokan hamayyarsa.

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune
Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune Hoto: Aleksy Witwicki/Sipa/picture alliance

A ranar Lahadi ne hukumar zaben Aljeriya ANIE ta sanar da sunan shugaban kasar mai ci Abdelmadjid Tebboune a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban hukumar zaben kasar Mohamed Charfi ya ce Abdelmadjid Tebboune ya lashe kashi 94% na kuri'u da aka kada, ya kuma kara da cewa mai nasarar ya samu kuri'u da yawansu ya kai 5,320,000 cikin kuri'u 5,630,000 da aka kada.

An fara kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Aljeriya

Taboune mai shekara 78 ya zama shafaffe da mai, abinda ya bashi damar samun nasara a kan babban abokin hamayyarsa Abdelaali Hassani mai shekara 57 da kuma dayan dan takarar Youcef Aouchiche mai shekara 41.

Shugaban hukumar zaben ya kuma ce an yi zabe babu murdiya kuma hakan ya nuna irin dattakun masu kada kuri'a.

Aljeriya ta dakatar da ayyukan raya kasa a Nijar

To sai dai kuma fa bai fadi adadin mutane da suka fita rumfunan zabe a hukumance ba, abinda dama ake ganin zai bai wa Taboune nasara.