1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Firaminista zai tsaya takara

Binta Aliyu Zurmi LMJ
November 21, 2021

Firaministan wucin gadi na kasar Libiya Abdulhamid al-Dbeibah ya yi rijista a matsayin dan takara a zaben shugaban kasa da ke tafe a watan Disamba.

Libyen Dbeibah wiedereröffnet die Straße Misrata - Sirte
Firaministan Abdulhamid al-Dbeibah yayin sake bude wata hanya a Buwairat al-HassounHoto: Mahmud Turkia/Getty Images/AFP

Wannan dai na zuwa ne bayan da a baya Abdulhamid al-Dbeibah mai shekaru 63 a duniya ya sha alwashin ba zai yi takara ba, matakin da ya ba shi damar darewa kujerar firaministan da yake kai a yanzu. Ana ganin wannan matakin shiga takarar da firaministan ya yi, ka iya janyo wani sabon rikici.

Da ma dai Firaminista al-Dbeibah na daga cikin masu adawa da dokar da kakakin majalisar dokokin Libiyan Aguila Saleh ya samar, na yin zaben a karshen wannan shekarar. Wannan zabe na Libiya na da matukar muhimmanci, inda ake fatan zai kawo karshen rikicin da kasar ta kwashe tsawon shekaru 10 tana ciki.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW