Abin da EU da AU za su tattauna a taronsu
February 17, 2022Shugabar hukumar gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta shirya domin ganin babu abin da aka bari a baya wajen taron tsakanin bangarorin biyu. Kwanaki gabanin ganawar, ta yi tattaki da jirgin sama domin fayyace komai ga Shugaba Macky Sall na Senegal wanda yake rike da shugabancin karba-karba na shugabannin Afirka, tare da alkawarin cewa Kungiyar Tarayyar Turai za ta samar da kimanin kudin Euro miliyan 150,000 domin fadada kayyayakin jin dadin rayuwa a nahiyar Afirka.
Ursula von der Leyen Shugabar hukumar gudanarwar ta Kungiyar Tarayyar Turai ta kara da cewa: "Muna aiki tare kan taro tsakanin Kungiyar Tarayyar Afirka ta Kungiyar Tarayyar Turai don shirya taron mai zuwa. Kungiyoyinmu biyu suna da manufa guda kan tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasa. Wannan taron, dole ya nuna hanya da yadda za a cimma manufar."
Takaici kan rawar Turai na karuwa a Afirka
A nahiyar Afirka, akwai ra'ayoyin mabanbanta da ke karuwa cikin 'yan shekarun da suka gabata kan dangantaka tsakanin nahiyoyin na Afirka da Turai. Farfesa Carlos Lopes na jami'ar Cape Town da ke Afirka ta Kudu ya ce rashin gamsuwa da dangantakar ke kara sa Afirka neman hanyar da nahiyar za ta samu ci-gaban masana'antu.
Carlos Lopes ya ce: "Me ya sa ake maganar zama irin na lokacin mulkin mallaka da Afirka ke samar da kayayyakin da ake sarrafawa, inda ba a sarrafa kayayyaki da yawa, sannan misali akwai yarjejeniyar kare muhalli ta Turai da ake tattaunawa gani da yanayin da ake ciki."
Babban misalin shi ne yadda kasashen Rasha da Turkiyya ke kara samun ta cewa a nahiyar Afirka, haka kuma sakamakon rashin samun wadatattun rigakafin annobar cutar coronavirus, Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya kwatanta yanayin da irin mulkin nuna wariyar launin fata da kasarsa ta fuskanta lokacin mulkin Turawa tsiraru na kasar. A baya dai Shugaban hukumar gudanarwar Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki ya gana kan batutuwa da Ursula von der Leyen Shugabar hukumar gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai.
AU na son EU ta yi la'akari da shawarwarinta
Nils Keijzer na cibiyar ci-gaba da Jamus ya ce babban abin yi shi ne samun matsaya tsakanin nahiyoyin biyu: Ya ce "Idan aka duba tasirin yanayin shugabannin Afirka da Kungiyar Tarayyar Afirka za su bukaci ci gaba da aiki da taswirar da aka tsara wajen aiwatarwa, sannan Tarayyar Turai tana bukatar samar da sabbin tsare-tsare da ra'ayoyi. Ina tsammani wani lokaci za a samu zaman zullumi kan dangantakar."
Ana sa ran taron kolin zai taimaka wajen warare wasu daga cikin sabanin tsakanin nahiyoyin na Afirka da Turai da ke makwabtaka da juna.