1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abin yi in ana zaton an kamu da Ebola

Adrian Kriesch / ASJanuary 14, 2015

Mafi muhimmanci shi ne a tuntubi likita

Ebola Screening JFK Flughafen USA
Hoto: picture alliance/Landov

Cibiyar Robert Koch da ke tarayyar Jamus ta fidda wasu matakai da za a iya amfani da su wajen gano ko ana dauke da cutar Ebola. Wadannan matakai kuwa su ne:

Dubawa ko mutum na da zazzabi (ko zafin jiki ya zarta maki 38.5 a ma’aunin Celsius) ko gudawa ko kulammo.

Za kuma a iya duba wadannan abubuwa:

Mara Lafiya

Idan mutum ya yi mu’amala da wanda ke dauke da Ebola, ko wanda ake zargin yana dauke da ita, ko wanda cutar ta hallaka tsakanin kwanaki 21 da cutar ke dauka kafin alamunta su bayyana.

KO

Idan mutum ya yi aiki a dakin gwaje-gwajen jini ko asibiti ko wani waje makamancin wannan, da zai sa mutum ya yi mu’amala da wanda ya kamu da cutar ko jini, ko wani ruwa na jikin mai dauke da ita kwanaki 21 kafin bayyanar alamu na farko na kamuwa da cutar.

KO

Idan mutum ya zauna ko ya ziyarci daya daga cikin kasashen da cutar ta bulla (Liberiya ko Saliyo ko Gini ko Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango) kwanaki 21 kafin bayyanar alamun farko na kamuwa da cutar ko kuma idan mutum ya ci naman daji kamar Jemage ko Biri ko kuma ya yi wata mu’amala da su.

Idan har daya daga cikin wadannan abubuwa ya faru to a sanar da likita ko cibiyar kula da lafiya da ke yankin da ake. Akwai kuma layukan waya na kar ta kwana da za a iya kira wanda ake da su a kasashen da cutar ta bulla, wanda da zarar mai cutar ya nema, jami’i zai yanke hukuncin irin matakan da za su dauka wajen kula da shi.

Yana da kyau a gane cewar baiwa jami‘an kiwon lafiya bayanai cikakku kana sahihai na da muhimmanci. Gano cutar da wuri kan taimaka wajen ceto ran wanda ke dauke da ita. A wannan gaba dole ne mai cutar ya kauracewa hada jiki da sauran mutane kamar gaisuwa da sumbata da jima’i.

Wani abu mai muhimmanci shi ne a gagguta kai jinin mai cutar ko yawu ko fitsari da aka dauka zuwa dakin gwaje-gwaje da ke da isassun kayan aiki don tabbatar da cewar ko akwai cutar ta Ebola ko kuma babu.