1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMasar

Abokin hamayyar al-Sisi ya jefar da kwallo a zaben Masar

Mouhamadou Awal Balarabe
October 13, 2023

Babban dan takarar adawa a zaben shugaban kasar Masar Ahmed al-Tantawi ya sanar da janye takararsa, watanni biyu gabanin kada kuri'a da ake ganin Shugaba Abdel Fattah al-Sissi mai ci zai lashe shi.

 Abdel Fattah al-Sisi na daga cikin 'yan takara hudu da ke neman shugabancin Masar
Abdel Fattah al-Sisi na daga cikin 'yan takara hudu da ke neman shugabancin MasarHoto: Sayed Hassan/dpa/picture alliance

Daraktan yakin neman zabensa ne ya sanar da cewa al-Tantawi bai yi nasarar tattara sa hannun 'yan kasa 25,000 da ake bukata don samun damar tsayawa takarar zaben shugabancin Masarba, duk da goyon baya da yake da shi a kasar. Sai dai an kama kimanin magoya bayan wannan tsohon dan majalisar mai shekaru 44 da haifuwa a lokacin yakin neman zabe. Sannan al-Tantawi ya zargi Jami'an tsaro da sanya na'urar leken asiri a cikin wayarsa.

Karin bayani: Jama'a sun kauracewa rumfunan zaben Masar

 Baya ga Shugaba Abdel Fattah al-Sissi da ya tattara sa hannun 'yan majalisa 424, 'yan takara uku da ba sa da karfin fada a ji ne za su yi zawarcin kujerar shugabancin Masar, ciki har da Farid Zahran da Abdel-Sanad Yamama da Hazem Omar. Daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Disamba ne al'ummar Masar za su kada kuri'a, amma  matsin tattalin arziki zai kasance babban batu a zaben kasar da kashi biyu bisa uku ke fama da talauci.