Abu Namu: Sana'ar talla a yankin Dandi
December 12, 2022Talla
Tun daga shekara hudu ne dai Dandawa ke fara dora wa diyansu mata talla a wani mataki na fara shirya auren diyansu saboda a wannan lokacin ne ko wacce uwar diya ke kokarin ganin ta fita kunya ta hanyar yi wa diyarta kayan daki da kuma yi wa 'yan uwan ango kaya na gani na fada. Wannan dai na daga cikin abubuwan da ke taka wa wasu yara 'yan mata birki a fanni karatu tare da lalata tarbiyarsu. Domin jin karin bayyani sai a saurari shirin daga kasa.