1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu: Mata da shafukan sadata zumunta

September 25, 2023

Mata masu aikawa da batun damuwarsu a kan kafafen sada zumunta domin neman shawara musammun a fannin zamantakewa.

Hoto: AMO - stock.adobe.com

A lokuta da dama a kan samu sakonnin da mata kan turawa masu shafukan sada zumunta domin bayyana matsalolinsu da nufin neman mafita ga dimbin mabiya wadannan shafukan, inda suke neman a sakaya sunansu. Daga nan kuma kowa sai fara tofa albarkacin bakinsa tare da bayar da shawara da ma mahangarsa ga wannan sakon. Sai dai ana ganin hakan tamkar tona wa kai asiri ne da kuma tallata sirrin cikingida.