Mata na fafutukar neman na dogaro da kai
July 12, 2021Talla
Tun dai a wancan zamanin da duniya ke kwance ake kiran mata da su kama sana'a. A kan ce rashin sana'a ga mace shi ke kawo yawan fadace-fadace tsakanin uwargida da mai gida, ta yiwu yawan bani-bani daga bangaren matar gida a kan kudin cefane ko kudin anko ko dai wani abu da ya shafi na hidimomin yau da kullum. Sai dai da dama na ganin an sami ci gaba sosai na yawaitar samun yawan sabani tsakanin ma'aurata saboda yadda mata a wannan lokacin suke fadi tashin ganin sun mayar da taro zuwa sisi wanda ke ba su damar dauke kananan dawainiya da ya shafe su ko 'ya'yansu, kuma matan ke cewa hakan ya sa mazajensu yin alfahari da su.