Abu Namu: Mata da zaben Najeriya
March 25, 2019Talla
Kamar yadda aka sani mata ba su tabuka wani abin a zo a gani ba a zaben Najeriya na 2019. Kadan daga cikin matan da suka nemi takara sun fadi zaben wasu ma ba su ma kai labari ba tun daga matakin farko. Amma wasu mata 'yan siyasa na cewa akwai sauran lokaci da za a iya aiwatar da gyara in har da gaske ake ana son a yi wannan tafiya da mata.