1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abubakar Shekau ya ce ba a koresu daga Sambisa ba

December 29, 2016

Jagoran Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon bidiyo inda ya musanta nasarar da gwamnatin Najeriya da jami’an tsaro suka ce sun samu na fatatakarsu daga daji Sambisa da ke jihar Borno.

Nigerien Boko Harams Führer Abubakar Shekau
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A wannan faifain bidiyon mai tsawon mintuna 24 an nuna Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau tsaye a gaban motoci kuma a tsakanin wasu mayakan Kungiyar dauke da makamai inda ya yi bayani cikin Larabci da Hausa. Wannan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Jami'an tsaro suka tabbatar da murkushe Kungiyar bayan karbe iko da babban sansaninsu da ke dajin Sambisa inda suke nuna cewa yaki ya zo karshe. Sai dai Abubakar Shekau ya ce suna nan inda suke, kuma yaki bai kare ba inda ya barazanar cewa za su ci gaba da kai hare-hren Kunar bakin wake.


Duk da cewa babu rubutaccen kwanan wata na ranar da aka nadi wannan faifain bidiyo, amma shugaban Kungiyar Boko Haram ya ce ranar Lahadi da ta gabata ne ya yi wadannan bayanai. Wadanda suka saba kallon sakon Kungiyar sun tabbatar da cewa mutumin da ya saba bayyana a matsayin shugaban Kungiyar shi ne a faifain, abin da ke nuna cewa akwai sauran rina a ka ba.
Sai dai akwai ‘yan Najeriya da suka nuna yarda da bayanan da gwamnatin da kuma Sojojin suka yi na cewa an samu nasara.

Shugaba Buhari da kansa ne ya sanar da karbe SambisaHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber


Sojojin Najeriya ma sun tabbatar da hakan inda suke shirin maida dajin sansanin horar da Sojoji da gwada makaman yaki, inda babban kwamandan rundunar yaki ta Lafiya Dole ya sanar da cewa sun kame ‘ya'yan Kungiyar da dama inda wasu kuma suka mika wuya da makamansu. Sannan rundunar sojin Najeriya ta ‘yanto mutane fiye da 1800 da suka hada da mata da yara kanana.

Sai dai rashin jin duriyar inda shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya shiga dama batun ko akwai 'yan matan Chibok da aka sace a mutanen da sojojin suka samu 'yantosu na zama babban al’amari kuma abin tambaya.