1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewa ta halaka yara a Ngala

Ramatu Garba Baba
August 13, 2021

Fashewar greneti ta yi sanadiyar rayukan wasu yara kanana a garin Ngala da ke jahar Borno a Arewa Maso Gabashin Najeriya. Garin ya sha fama da ayyukan Boko Haram.

Nigerianischer Soldat
Hoto: FLORIAN PLAUCHEUR/AFP

Fashewar greneti ta yi sanadiyar rayukan wasu yara biyar a garin Ngala da ke jahar Borno daf da iyakar Najeriya da jamhuriyyar Kamaru. Wani mazaunin garin mai suna Umar Kachalla, ya sheda wa kamfanin Labaran Faransa AFP cewa, yaran sun dauki abin fashewar suna wasa da shi, ba tare da sun san ko mene ne ba, inda tsatsauyi ya ja abin ya fashe a hannunsu. Akwai wasu da suka ji rauni a sakamakon fashewar. 

A shekarar 2014, mayakan Boko Haram suka karbe ikon Ngala da cibiyar kasuwancin nan ta Gamboru duk a jahar ta Borno, kafin daga baya rundunar sojin Najeriya ta sake karbe garuruwan daga hannun kungiyar a shekarar 2015, amma mayakan sun bar tarin abubuwan fashewa da suka dasa a duk wuraren da suka zauna a wancan lokacin, mutane da dama sun rasa rayukansu wasu sun ji rauni a sakamakon fashewar da aka yi ta samu bayan fatattakarsu, yawancin mamatan yara ne kanana.