Abubuwan sha'awa da ban al'ajabi a gasar AFCON
January 14, 2026
Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar ta Afirka CAFPatrice Mostepe ya kasa boye jin dadinsa da wadannan abubuwa da suka dauki hankali a gasar ta AFCON da ke gudana a Moroko:
"Za a kwashe shekaru da dama duniya na jinjina a abubuwan birgewa da ke faruwa a wannan gasar da ta shiga tarihi. Kama daga zakulo mana sabin 'yan wasannin da ke boye gami da kaddamar da sabbin salon ziga 'yan wasa da kuma tarin ribar da mahalarta gasar ke samu, wajen huce haushinsu da huce zakatu gami da kashe kwarkwatar ido da ganin sabbin filayen".
Wasanni tamkar kana Turai, gami da karin yawan kungiyoyin wasanni da karin kudin tukuicin da wadanda suka lashe kambun za su samu da zai kai dala miliyan 10 a bana. Wala Allah gwarzo mafi fice a gasar da har wasu suke cewa shi yafi cancanta a ma bashi kambun gasar, duk da ko buga kwallo ko da sau daya a yayin gasar ba, shi ne Michel Kuka da kewa kansa inkiya da Lumumba, tsohon shugaban kasarsa ta Kwango da turawan mulkin mallaka suka yi wa kisan gilla a shekarar 1961.
Shi dai Lumumba ya fito da wani salon ne a bana na ziga 'yan wasan kasarsa ta hanyar kamewa tamkar gawa hanunsa sama har na tsawon mintina 90 ko fiye da haka, a duk lokacin da kasarsa ke buga wasa gawa don karawa 'yan kasarsa kuzari kan sadaukar da kai.
Baya motsi ko rike wata tuta duk da kade-kaden da raye-rayen da wadanda ke kewaye da shi suke yi. Sai a ranar da Aljeriya ta cire kasarsa ne bayan mintina 110 yana kame, ya motsa don cire tabaraudinsa da nufin goge hawayen nuna takaicin buge kasarsa da aka yi.
Sai dai bayan wasan Lumumba ya sami gayyata daga tawagar Aljeriya domin rarrashinsa da kuma bashi hakuri kan cin fuska da zolayar da wani dan wasan kasar ya yi masa, a kan lokaci ya yi yanzu ya fadi kasa tunda an doke kasarsa. Duk wani yunkurin rarrashi da lallamar da akai ta mai kan ya zauna a Moroko har sai an gama gasar baki daya a madadin dala dubu biyu da za a dinga bashi duk rana ya ci tura.
To sai dai shi ma dan wasan Najeriya ya daukar wa Lumumban fansa a ranar da Najeriya ta doke Aljeriya da ci biyu da nema, yadda shi ma ya kwaikwayi Lumumba wajen kamewa irin tasa don yi mar jinjina. A kasar Mali kuwa, dubun wani malamin tsubbu mai suna Karamoko Sinayoko ce ta cika, wanda ya karbi makudan kudi a hanun jami'an kwallon kafan kasar a madadin layu daya ba su gami da alkawarin dawowarsu gida da kambun gasar.
To sai dai bayan da Senegal ta doke Malin da ci daya mai ban haushi, jami'an tsaro sun damke bokan bayan da ya ki dawo da kudin kafin alkalami da aka bashi, yana mai dagewa kan cewa shi ne ma yake bukatar a cika masa sauran ladansa:
"Kasar Mali bata bina ko anini.Ni ne nake ma bukatar sauran kudin aikina. Ai kowa ya san cewa, biyan bukata na hanun Allah ne kadai."
A Nageriya ma, attajiri Abdul Samad Rabiu ya yi alƙawarin ban mamaki don ƙarfafa Super Eagles a wasan Afcon. Ya shaida alƙawarin dala dubu 500 ga ’yan wasan idan sun ci nasara a wasan semi-final, tare da ƙarin dala dubu 50 ga kowace kwallo da suka zura a wasan. Idan kuma har suka lashe kambun gasar, to zai ba su dala miliyan guda tare da dala dubu 100 ga kowane kwallo da aka zura a wasan karshe.