1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Boko Haram ce ta fasa gidan kason da ke Abuja'

July 6, 2022

Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta Najeriya ta ce 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai harin domin kubutar da mambobinsu da ke tsare a gidan kason.

Nigeria Sicherheitsbeamter am Hochsicherheitsgefängnis in Kuje
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Kusan fursunoni 900 kawo yanzu hukumomi a Najeriya suka tabbatar sun tsere daga gidan yarin Kuje da ke babban birnin kasar, Abuja bayan harin da aka kai a ranar Talata da daddare. Mai magana da yawun hukumar da ke kula da gidajen yarin kasar, Umar Abubakar, ya  tabbatar da cewar wasu daga cikin fursunonin yanzu haka na hannun hukumomi. To amma ya ce kawo yanzu fursunoni 443 ne  ba a ji duriyarsu ba. 

Da yammacin Larabar nan, Shugaba Muhammadu Buhari, ya kai ziyara gidan kason na Kuje, inda aka nuna masa irin mummunan ta'adin da maharan suka yi kafin su saki fursunoni. Tun da farko gwamnatin Najeriyar ta zargi kungiyar Boko Haram da kai harin ta amfani da abubuwa masu fashewa domin kubutar da mambobinsu da ke wurin.

A baya dai an sha samun irin wannan a Najeriya. To amma wannan shi ne karon farko da mahara suka fasa gidan yari a babban birnin kasar, Abuja.