2023: Wakilan jam'iyyu sun yi dandazo a Abuja
May 19, 2022Wadannan 'yan siyasa da ke zama wakilan da za su zabi wadanda za su yi wa jam'iyyunsu takara sune a yanzu tutarsu ke kadawa a fagen siyasar Najeriyar, domin suke rike da sandar duka ta zaba wa kasar makoma.
A baya dai yunkuri na kawar da amfani da wakilai a zaben fitar da gwani ya kasa samun nasara, abin da ya sanya su zama wadanda a yanzu ake masu kallon masu rike da akalar siyasar kasar kafin aje babban zaben shekara mai zuwa. Yawaitarsu a birnin Abuja, ta sanya tuni manyan otel-otel suka zama matattara ta 'yan siyasa, inda 'yan takara ke bin su suna kamun kafa. Ana kuma zargin amfani da kudade a kokarin samun goyon bayan 'delegate' din a dukkanin manyan jam'iyyun kasar.
A bana ne dai Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya rattabu hannu kan dokar zabe, wacce ake sa ran za ta samar da gyare-gyare a wurin zaben fitar da gwani. To ko hakan za ta samar da sauyin da ake bukata a yanzu da ake 'yan kwanaki kafin a fara zaben fitar da gwanin?
Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta bukaci jam'iyyun kasar su kammala zabukan fitar da gwanin nan da makon farko na watan Yuni mai kamawa.