Matakin hana adaidaita sahu a Abuja
November 13, 2019To wannan lamari dai ya sanya ta da hatsaniya da kura da ma rudani, saboda haramta amfani da keke Napep din a tsakiyar birnin Abujan da manyan hanyoyi bisa sabon mataki na hukumar kula da birnin. Duk inda ka bi zaka ga fayau babu masu Keke Napep din, kasancewar sun koma aiki a unguwanni da kuma inda ake da rukunin gidaje da suke a killace. A cewar jami'in yada labarai na ministan Abujan, Mallam Abubakar Sani wannan doka ta haramcin fa ba sabuwa ba ce. Tuni dai masu tuka keke Napep din suka nuna bacin ransu da wannan mataki da suka ce na barazanar jefa su cikin rashin aikin yi, domin akwai masu wannan sana'a sama da dubu 20 a Abujan da suka dogara a kanta.
A tabakin shugaban direbobin Keke Napep din ko adaidadata sahu a Abuja Musa Ibarahim Anchau matakin ya jefa su cikin mawuyacin hali. Daukar matakin dakatar da tuka keke a unguwanin da dama a matsayin yajin aiki, ya haifar da walhalu, domin mutane da dama sun taka da kafarsu zuwa wurare masu nisa saboda rashin keken a unguwaninsu. Abin jira a gani shi ne yadda wannan matakin da aka dauka a kan direbobin adaidata sahun zai kasance a Abujan fadar gwamnatin Najeriya, a matsayin hanya ta tsaftace tsarin sufuri da tsaro da ma zamantakewar al'umma da gwamnatin ke dagewa a matsayin dalilanta na yin hakan.