Abzunawa sun kaurace wa tattaunawa a Mali
September 10, 2020Gamayyar kungiyoyin tawayen Abzinawan Mali ta CMA ta yanke shawarar kaurace wa zaman shawarwari da kwamitin mulki sojin kasar ya shirya, don shata hanyoyin da za a bi wajen mayar da mulki a hannu farar hula. A lokacin da yake wa manaima labarai bayani, Kakakin wannan gamayya, Almou Ag Mohamed ya ce wannan mataki na su ya biyo bayan rashin la'akari da damuwarsu, kuma ba a yi zaman tattaunawar shara fage da jami'an mulkin soja kamar yadda aka shirya tun farko ba.
.Daruruwan shugabannin siyasa da na kungiyoyin kwadago da na kungiyoyin farar hula ne suka hallara a birnin Bamako, don kayyade tsawon lokaci da za a yi na rikon kwarya da kuma wanda ya kamata ya shugabancin kasar tsakanin farar hula da soja. Amma babban malami addinin Musulunci na na kasar ta Mali, Imam Mahmoud Dicko ya bukaci gwamnatin mulki soja ta kasar ta ta sakar wa fararen hula ragamar tafiyar da kasar da kuma nada firamanista.