Action Aid ta zargi G8 da rashin cikwan alkawali
May 30, 2007Ƙungiyar bada agaji ta Action Aid, ta bayyana sanarwa a game da tallafin da ƙasashe masu karfin tattalin arziki ke baiwa ƙasshe matalauta.
Action Aid ta yi suka da kakkaussar halshe ,ga ƙasashen G8 a game da rashin cikwan alƙawali.
Ƙungiyar ta bada misalin taron shekara da ta gabata a ƙasar Britania, inda su ka alƙawarta yafe bassukan da su ka tambayo ƙasashe 35 mafi talauci a dunia, da kuma ware ƙarin dalla milion dubu 50, don talafawa wannan ƙasashe su yaƙi talauci, a tsukin shekaru 4 masu zuwa.
Ya zuwa yanzu, babu ɗaya daga wannan alƙawura, da ƙasashen G8 su ka cika, inji Action Aid.
Bugu da ƙari a shekara ta 2006,taimakon raya ƙasa ya ragu da dalla milion dubu 6, idan a ka kwatanta da shekarun baya.
Kamin taron G8, da zai gudana a Heiligendamm a nan ƙasar Jamus, mako mai zuwa,Action Aid ta yi kira ga shugabanin ƙasashe 8 mafi arziki a dunia,da su kasance masu cikwan alƙawali.