1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Adadin mahajjatan Masar da suka mutu a Saudiyya ya kusan 700

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 23, 2024

Tuni dai mahukuntar Masar din suka kwace lasisin kamfanonin tafiye-tafiye guda 16 na kasar

Hoto: Rafiq Maqbool/AP Photo/picture alliance

Adadin mahajjatan kasar Masar da suka mutu a Saudi Arebiya sakamakon tsananin zafi ya karu zuwa 672, yayin da ake ci gaba da neman wasu 25 da har yanzu ba a san inda suke ba, kamar yadda hukumokin kasar suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Karin bayani:Saudiyya ta kare mutuwar sama da mutum 1,000 saboda tsananin zafi

Tuni dai mahukuntar Masar din suka kwace lasisin kamfanonin tafiye-tafiye guda 16 na kasar, sannan suka mika su hannun mai gabatar da kara na kasar, don gurfanar da su gaban shari'a, bisa zarginsu da hannu wajen mutuwar alhazan, sakamakon jigilar alhazan da hukumomin kasar ba su tantance ba.

karin bayani:Masar za ta dauki nauyin taron sasanta rikicin Sudan

Firaministan Masar Mostafa Madbouly da ke jagorantar kwamitin binciken, ya shaida cewa mutane 31 ne kadai aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon jinyar rashin lafiya mai tsanani, daga cikin wadanda aka yi wa rajistar tafiya aikin hajjin a hukumance.