Adadin masu zanga-zanga a Girka na karuwa
February 12, 2012'Yan sandan Girka sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga a farfajiyar majalisar dokokin kasar, inda wakilan majalisar ke shirin kada kuri'a a kan sabbin matakan tsuke bakin aljihun da shugaba Lucas Papademus ya gabatar musu.
'yansandan sun ce akalla masu bore dubu 15 suka kewaye majalisar, inda wakilan suka fara mahauwara yau da rana, a yayinda a wasu dubu 10 suka yi dandazo a dandalin Omonia wanda bai da tazara sosai daga majalisar.
Wannan zanga-zanaga, ya hada da kungiyoyin 'yan kasuwa, da kuma matasa wadanda suka yi askin kwal kobo suna fifita tutocin Girka, da kuma masu ra'ayin gurguzu da mabiyansu wadanda suka rufe fuskokinsu.
Masu zanga-zangar dai sun yi Allah wadai da abunda suka kira yaudara wanda kungiyar Tarayyar Turai da Asusun bada lamuni na duniya da babban bankin Turai suke so su yi ma kasar ta su.
A lokacin da ya bude taron 'yan majalisar Ministan kudin Girka Evangelos Venizelos ya ce yanma da mahimmancin gwamnatin ta sami goyon bayan wannan shirin domin ta samu kaso na biyu na euro milliyan 130 wanda aka alkawarta mata.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala