1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu mutuwa sakamakon kamuwa da cutar Sida ya ragu

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
July 16, 2019

Hukumar yaki da cutar Sida ta duniya ta ce adadin mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar ya ragu fiye da yadda aka gani a shekarar 2017 a yankunan Kudanci da Gabashin Afirka.

Mosambik Friedliche Demonstration
Hoto: Ismael Miquidade

Wani rahoton da hukumar yaki da cutar Sida ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya yi nuni da cewa akalla mutane dubu 770 000 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Sida a shekarar bara, adadin da ya ke zama mafi karanta ga alkaluman rahoton da hukumar ta fitar a shekarar 2017. 

Raguwar mutuwar ya faru ne bisa samun magani akai-akai da masu cutar da ake samu a kasashen Gabashi da Kudancin Afirka, yankunan da wadanda suke dauke da SIDA suka kusa ribanya wadanda suke da ita gida biyu a duniya.

Rahoton ya ce kuma a yankin Turai ta gabas, da yankin Asiya ta Tsakiya, mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar sun kai kishi 29% a yayin da yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, masu dauke da cutar suka kai kishi 5% daga shrekarar 2010.