1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Adadin mutane da ambaliya ta halaka a Myanmar ya kai 226

September 17, 2024

Mutanen sun rasu ne sakamakon galabaita daga guguwar Yagi da ta yayyaga muhallansu.

Guguwar Yagi a Myanmar
Guguwar Yagi a MyanmarHoto: Myanmar Fire Service Department/Handout via Xinhua/picture alliance

Adadin mutane da suka rasa rayukansu sakamakon guguwar Yagi mai dauke da ruwa da iska ya karu zuwa 226 a ranar Talata.

Kafar yada labarai ta kasar Myammar ta ruwaito cewa mummunar guguwar mai dauke da ruwan sama ta rika kadawa a wasu sassan kasar.

Sabbin alkaluman na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yawan mutane da za su bukaci taimako za kai 630,000.

Shekara guda bayan ambaliyar ruwa a Libiya

Guguwar ta Yagi ta karade arewacin kasar Vietnam da Laos da Thailand da kuma Myanmmar sama da mako guda inda ta rika kadawa da ruwa mai karfin gaske.

Hukumomi sun bayyana cewa iftila'inta ya kashe sama da mutum 500 a kasashen da ta ziyarta baya ga ambaliyar da ta haddasa.

Birnin Maiduguri ya fuskanci ambaliyar ruwa

Mutum 77 sun bace ana can ana nema, baya ga 226 da suka rasu a cewar gidan talabijin na kasar. Ambaliyar ta kuma haddasa mummunar asara ga dubban hektan gonakin shinkafa.