Mutanen da suka rasa rayukansu a ibtila'in Myammar ya karu
March 29, 2025
Girgizar kasar mai karfin maki 7.7 a ma'aunin richter ta auku ne a kudu maso yammacin Sagaing a tsakiyar Myanmar, wanda iftila'in ya yi sanadiyar rayukan mutane sama da 1,000 wasu mutanen 1,670 da suka sami raunuka baya ga wadanda ke makale a baraguzan gini.
Shugaban mulkin sojin kasar Min Aung ya yi kira ga kasashen duniya da su kai musu dauki.
Da safiyar wannan rana ta Asabar ce mahukunta a kasar Indiya sun aike da babban jirgin sama makare da kayayakin agaji ga al'ummar Myammar da iftila'in girgizar kasa ya same su a jiya Juma'a.
Iftila'in da ke zama mafi girma da kasar Myammar ta taba gani, ya lalata gidaje da ruguza gadoji tare ma da shafar wasu yankuna da ke da nisan sama da kilomita 100 daga inda lamarin ya auku.
Karin bayani: Girgizar kasa a Myanmar da Thailand