Adadin 'yan gudun hijira masu zuwa Turai zai karu
September 18, 2015Talla
Hukumar ta ce adadin 'yan gudun hijirar da ke kwararowa zuwa nan Turai zai karu nan gaba cikin 'yan kwanaki masu zuwa, kuma hanyoyin da 'yan gudun hijirar suke bi za su kara yawaita. A wani taron manema labarai da ya jagoranta, kakakin hukumar 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya Adrian Edwards, ya ce taron Hukumar Tarayyar Turai da zai gudana a ranar Laraba mai zuwa, zai kasance wata babbar dama ta nema wa wannan matsala mafita, inda ya ce wannan zaman taro zai kasance tamkar wata dama ta karshe, ganin yadda Tarayyar Turai ta kasa daukan matakai kan matsalar da tun farko ake iya ciyo kanta.