1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adama Barrow ya bukaci sojin ECOWAS su zauna

January 26, 2017

Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya bukaci sojojin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO su ci gaba da zama a kasarsa har zuwa watanni shida nan gaba domin tabbatar da tsaro da dorewar zaman lafiya a kasar.

Gambia Ankunft Präsident Adama Barrow in Banjul
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Sabon shugaban kasar Gambiya Adama Barrow da ya tsere zuwa kasar Senegal domin gudun abin da kaje ya zo wanda kuma aka rantsar da shi a ofishin jakadancin Gambiya da ke Dakar babban birnin kasar Senegal a ranar 19 ga wannan watan na Janairu, ya yanke shawarar komawa kasarsa a awannan Alhamis din, mako guda bayan rantsar da shi, kana kwanaki biyar bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jameh da ya kawashe sama da shekaru 22 a kan karagar mulki ya tafi gudun hijira zuwa Equatorial Guinea. A hirarsa da manema labarai, Halifa Sallah da ke zaman kakakin sabon shugaban kasar na Gambiya Adama Barrow ya tabbatar da batun komawar Baroow.


"Ya shaida min kwanaki biyu da suka wuce cewa zai iso a wannan Alhamis din, sai dai baya son a yayata dawowar tasa. Ya kuma mika godiyarsa ga wadanda suka taimaka wajen tabbatar da ganin an samu dai-daito cikin kwanciar hankali, a rikicin siyasar da ya nemi ya kunno kai a kasarmu."

Hoto: Getty Images/A.Renneisen

Tun dai a makon da ya gabata ne sojojin kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS ko CEDEAO suka isa kasar ta Gambiya da nufin tabbatar da tsaro bayan ficewar Jammeh. Rahotanni sun nunar da cewa Mr Barrow ya bukaci da a tsawaita zaman dakarun na ECOWAS ko CEDEAO a kasar. Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan wannan batu, jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Afirka ta Yamma Mohammed Ibn Chambas cewa ya yi:


"Abin da zan iya shaida muku a wannan lokaci shi ne, shugaban Gambiya ya bukaci dakarun ECOWAS su ci gaba da zama a Gambiya har nan da watanni shida masu zuwa, sai dai ya rage ga kungiyar ta ECOWAS ko CEDEOA ta samu lokaci domin ta yanke shawara akai."

Hoto: picture alliance/AP Photo/S.Cherkaoui


Abin da kowa ka iya tambaya dai shi ne mai ya hana Adama Barrow koma wa gida duk kuwa da cewa tun a karshen makon da ya gabta ne tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya sauka daga kan karagar mulkin da a baya ya yi kememe, tare kuma da ficewa daga kasar zuwa kasar Equatorial Guinea domin neman mafaka? Thomas Volk na gidauniyar Konrad-Adenauer ta Jamus a Senegal, cewa ya yi:

Hoto: Reuters/A. Sotunde


"Senegal na zaman wata abar koyi ce ta fuskar demokaradiyyya a Afirka ta yamma, ta samu ci gaba sosai a wannan fanni. A yanzu abin da ya rage wa sabuwar gwamnatin ta Gambiya shi ne kokarin hada kan al'ummar kasarta da kuma samar da Gambiyar da ta ci gaba." 

 

Hoto: Reuters/T. Gouegnon

Akwai damuwa kan cewa sai da aka yi wa Yahya Jammeh wasu alkawura da suka dangancí cewa babu wanda zai nemi bincikarsa bayan ya bar kan karagar mulki, kafin ya amince ya fice zuwa kasar ta Equatorial Guinea, abin da kuma Ibn Chambers ke cewa:


"Mr. Jammeh a matsayinsa na tsohon shugaban kasar Gambiya na da 'yancinsa da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi, kana kuma yana da hakkokin da ya kamata ya sauke kamar yadda kundin tsarin mulkin Gambiyan ya tanada."

Daruruwan mutane ne dai suka yi cincirundo domin yi wa sabon shugaban kasar tasu Adama Barrow maraba.