1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da ci gaba da tsare Nasiru El-Rufa'i

July 9, 2026

Magoya bayan tsohon gwammnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai sun fara bugun kirjin cewa tsare shi da hukumomin kasar ke yi na tsawon watanni ya kara wa dan siyasar farin jini

Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai Hoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

Yayin da ake dab da fara gangamin yaƙin neman zaɓen 2027 a Najeriya, babban jigon jam'iyyar ADC a Jihar Kaduna kuma tsohon gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa'i yana ci gaba da kasancewa a hannun hukumomi bisa wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.

Sai dai tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: shin tsarewar za ta rage tasirinsa a cikin jam'iyyar ADC, ko kuwa har yanzu zai ci gaba da taka rawa a siyasar Kaduna?

Bayan shafe watanni a hannun hukumomi, wasu jiga-jigan jam'iyyar ADC a Kaduna na ganin cewa Malam Nasiru El-Rufa'i zai ci gaba da kasancewa babban ginshiƙi a jam'iyyar duk da halin da yake ciki.

Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar, Hajiya Hafsat Mohammed Baba, ta bayyana cewa El-Rufa'i yana da dimbin magoya baya a kananan hukumomi 23 na jihar, kuma hakan na nuna irin karɓuwar da yake da ita a tsakanin al'umma.

Ta ce tun bayan kama shi da hukumomin ICPC da EFCC suka yi, da kuma yadda ake gabatar da shi a gaban kotu a kullum yana samun dubban jama'a da ke nuna masa goyon baya.

A nasa bangaren, ɗan gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya Comrade Abdul Bako, ya ce ko yana tsare ko ba ya tsare, Malam Nasiru El-Rufa'i na da ƙarfin tasiri a siyasar Kaduna.

Comrade Abdul Bako ya ƙara da cewa tsarewar da ake yi masa na iya ƙara masa karɓuwa a idon wasu mabiyansa, saboda yadda suke kallon lamarin.

A halin yanzu kuma, iyalan tsohon gwamnan na ci gaba da neman a ba shi beli domin samun damar kula da lafiyarsa. Haka kuma, wasu ƙungiyoyin farar hula da masu rajin kare dimokuraɗiyya na kira ga hukumomi da su gudanar da shari'ar cikin adalci tare da mutunta haƙƙinsa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani