Adawa da kauracewa biyan haraji
February 22, 2008Talla
Wata ƙungiya da ke adawa da batun zama na bai ɗaya a duniya, ta yi kira da a samar da wasu hanyoyi na hana kauracewa haraji a duniya. Kungiyar mai suna Attac ta yi wannan kira bayan rikicin haraji da ke gudana yanzu haka tsakannin kasar Jamus da 'yar karamar daula ta Leischtenstein, inda manya masu hannu da shuni nan Jamus ke boye kudadensu domin gujewa biyan haraji . Wani masani kan harkokin haraji Sven Gielgold na kungiyar Attac ya ce idan har da niya, akwai matakai da dama da kampanonin kudi na duniya zasu iya dauka na hana magudin haraji. Amma tambaya a nan shi ne? A shirye ƙaashen da abin ya shafa suke wajen daukan matakan dakatar da magudin haraji? nan batu ne na zuci, babu shakka daukan wadannan matakai na iya kawo matsaloli daban daban, amma ya kamata kasashen das abin ya shafa su dage kan abin da suka saka gaba domin cimma burinsu. Gielgold ya kara da cewa. Mataki na farko da ya kamata a dauka nan shi ne, toshe hanyoyi na tura kudi zuwa wadannan dauloli da ke karbar haramtattun kudade. Na kuwa shi ne kara yawan ma'aikatan haraji tare da tilasta bankuna gabatar da bayanai kan masu ma'amala dasu. Bugu da kari, ya zama tilas ga kowa ya rika harkokin harajinsa a bayyane ba tare da wani siri ba. Gielgold ya kara da cewa: Yana da mahinmanci a san a wadanne kasashe ne kampanoni ke da kanannan ofisoshinsu, nawa suke samu? kuma harajin nawa suke biya. Giegold ya kara da cewa, kamata yayi Jamus ta yiwa Kungiyar Tarryyyar Turai barazanar cewar bazata sake biyan kudin shiga na kungiyar ba idan har bankuna basu daina daukan matakan boye a harkokin ajiya ba. Bazamu sake barin wasu kasashe na kwaruwanmu wajen biyan kudaden shiga ba, dole ne kamar yadda wasu kamar kampanonin kera motoci, da na hada magungunna har ma da na manoman kasar Faransa suka tashi tsaye suka kare makomar kansu daga kungiyar, tare da kasar Britaniya da ta ki yin karbar wasu ka'i dojin EU wadanda ta ce basu dace da irin rayuwar al'umarta ba, ya kamata mu ma mu ki biyan kudin shiga ga EU har sai an biya mana namu bukatu. Daman Jamus ce ke biyan haraji mafi tsoka ga kungiyar ta EU. Shi ma wani tsohon sakatare janar na jam'iyar CDU kuma babban jami'in kungiyar Attac Heiner Geißler ya yi suka game da yadda harkokin haraji ke tafiya, tare da cewa ba kawai keta dokar biyan haraji na shugaban kungiyar kampanin aika wasiku na Jamus Klaus Zumwinkel ne babban matsala da ake fuskanta a game da kaucewa biyan haraji nan Jamus ba.
Talla