1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ADC: Kotu ta amince da shugabancin David Mark

Uwais Abubakar Idris
July 3, 2026

Yayan jamiyyar adawa ta ADC a Najeriya na murna bayan da babbar kotu da ke Abuja ta yanke hukuncin da ya hallata shugabancin Sanata David Marka da mukarrabansa a jamiyyar

Babbar kotun tarayya da ke Abuja
Babbar kotun tarayya da ke AbujaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Wata sabuwar fata ce ta sami jamiyyar adawa ta African Democratic Congress ADC bisa ga wannan samun tabbaci na shugabancin Sanata David Mark bayan kwashe lokaci mai tsawo ana fafatawa a kotu. Alkalin babbar kotun da ke Abuja da ya tabbatar da wannan yace tun farko ma wannan kara bata da dalilin saurarenta domin lamari ne da ya shafi batun cikin gida na jamiyyar. 

Taron 'ya'yan Jam'iyyar ADC a AbujaHoto: Uwaisu Abubakar Idris/DW

Sabon babi ne ga yayan jamiyyar ta ADC da ta shiga halin rashin tabbas na kila wa kala a kan zaben 2026 duk da cewa ta yi ta maza na ci gaba da shirye-shirye. Ko me suka sanya a gaba a yanzu musamman da zaben 2027 da suke son karbe mulki a hannun jamiyyar APC mai mulki? 

Tsllake suradi na rashin tabbas ne ga ilahirin ‘yan takarar a karkashin jamiyyar ta ADC, domin su ne suka fi murna da wannan hukunci na kotu da a yanzu ya basu dama ta kara azama a fafutukar da suke yi, sanin cewa lokaci na kara kure masu.

Taron 'ya'yan Jam'iyyar ADC a AbujaHoto: Uwaisu Abubakar Idris/DW

Jamiyyar adawar Najeriya ta ADC na cikin jamiyyun da suke fama da rigingimu a kataniyar da suke yi na kalumbalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu a jamiyyar da ke mulki a Najeriyar ta APC. Ta kai matakin da dukkanin manyan jamiyyun kasar na fsukantar shari'u a kotu. Dr Abdurrahman Abu Hamisu masanin kimiyar siyasa ne da ke jami'ar Abuja ya bayyana tasirin hukuncin kotun na hallasta shugabancin Sanata David Mark ga jamiyyar da ADC..

Hukuncin kotun dai ya sake zaburar da yan siyasa da guguwarta ke kadawa musamman neman kwace mulki da jamiyyun adawar ke yi daga hannun shugaba Tinubu na jamiyyar APC mai milki a Najeriyar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani