1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Adeleke ya lashe zaben gwamnan Osun

August 16, 2026

Hukumar Zaben Najeriya INEC ta ce Adeleke na jam'iyyar Accord ne ya yi nasara bayan ya doke abokin hamayyarsa na APC.

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke
Gwamnan jihar Osun Ademola AdelekeHoto: Osun Government House

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake lashe zaben gwamna, inda zai ci gaba da jagorantar jihar na tsawon shekara hudu bayan ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC.

Sakamakon da Hukumar Zaben Najeriya (INEC) ta sanar ya nuna cewa Adeleke ya samu kuri'u 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu kuri'u 444,815. Dan takarar jam'iyyar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da kuri'u 17,180.

Wannan nasara na da muhimmanci ga gwamna Adeleke saboda ya lashe zaben ne karkashin jam'iyyar Accord, bayan ya fice daga jam'iyyar PDP a watan Disamba, wadda ya lashe zaben gwamna a karkashinta a wa'adinsa na farko.

A lokacin da ya sauya sheka Mista Adeleke ya bayyana cewa manufar jam'iyyar Accord ta fi dacewa da abin da gwamnatinsa ta sanya a gaba na inganta walwalar al'umma da ma'aikata.

Ana fargaba a Osun kan zaben jihar na makon gobe

An gudanar da zaben ne cikin tsauraran matakan tsaro bayan watanni na yakin neman zabe da zarge-zargen neman tayar da hankali tsakanin 'yan siyasa da manyan jam'iyyu.

Da safiyar ranar zabe, Adeleke ya kada kuri'arsa a mazabarsa da ke Ede North, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai sake lashe zaben.

A lokacin kuma, masu sa ido sun ce an fara kada kuri'a cikin lumana a sassa da dama na jihar duk da wasu korafe-korafe kan matsalolin kayan zabe a wasu wurare.

Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Muhimman abubuwa biyar kan zaben

An gudanar da zaben a kananan hukumomi 30
An gudanar da zaben gwamnan Osun a dukkan kananan hukumomi 30 na jihar da kuma rumfunan zabe 3,763. Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta jibge ma'aikatanta da kayan zabe a fadin jihar domin gudanar da zaben.

Sama da mutum miliyan 1.9 suka karbi katin zabe
INEC ta bayyana cewa mutane miliyan 2.3 ne ke cikin rajistar masu zabe a Osun, amma mutum 1,906,390 ne suka karbi katin zabe na dindindin wato (PVC), wanda ya ba su damar kada kuri'a a zaben.

'Yan takara 15 ne suka fafata
Jam'iyyu 15 ne suka gabatar da 'yan takara domin neman kujerar gwamnan Osun. Sai dai fafatawar ta fi zafi ne tsakanin Ademola Adeleke na Accord da Bola Oyebamiji na APC da Najeem Salaam na ADC.

INEC ta daura sakamakon a IReV
Bayan an fara kirga kuri'u, INEC ta fara daura sakamakon da aka samu a rumfunan zabe a shafinta na IReV domin jama'a su rika bibiyar sakamakon kai tsaye. A yayin da ake ci gaba da tattara alkaluma, dubban sakamakon rumfunan zabe ya riga ya isa a shafin na INEC.

An yaba da zaman lafiya a yawancin wuraren zabe
Masu sa ido kan zabe sun ce an kada kuri'a cikin lumana a mafi yawan rumfunan zabe da suka sa ido a kansu, duk da cewa an samu rahotannin sayan kuri'u da matsalolin na'urar BVAS a wasu wurare.

Najeriya: 'Yan adawa sun farfado da batun takara daya tilo a 2027

Hoto: Yasuyoshi Chiba/AFP

Abubuwa da suka faru kafun zabe

Kafin zaben, an shafe watanni ana yakin neman zabe tare da zarge-zarge tsakanin manyan jam'iyyun siyasa. Hakan ya sa jami'an tsaro suka kara tsaurara matakan tsaro a fadin jihar domin tabbatar da zaman lafiya.

Shugaba Bola Tinubu ya umurci Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Tunji Disu, da sauran shugabannin hukumomin tsaro su tabbatar da an samar da isasshen tsaro a rumfunan zabe tare da hana duk wani yunkurin tayar da zaune tsaye.

Kwanaki kadan kafin zaben, Hukumar EFCC ta kulle asusun gwamnatin Jihar Osun, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Sai dai daga bisani Shugaba Tinubu ya umarci hukumar ta bude asusun, yana mai cewa lokacin daukar matakin bai dace ba, musamman kasancewar ana daf da gudanar da zaben gwamna.

Hoto: Osun Government House

Abin da Adeleke zai mayar da hankali kai a wa'adi na biyu

  • Kammala manyan ayyukan tituna da gadoji da gwamnatinsa ta fara.
  • Inganta ilimi, ta hanyar ginawa da gyaran makarantu tare da daukar karin malamai.
  • Kara inganta harkar lafiya, musamman cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da asibitocin gwamnati.
  • Kirkirar ayyukan yi ga matasa da mata ta hanyar tallafa wa kananan sana'o'i.
  • Inganta walwalar ma'aikata da masu karbar fansho, inda ya yi alkawarin ci gaba da biyan albashi da fansho a kan lokaci.
  • Karfafa noma da bunkasa tattalin arzikin jihar, domin jawo karin masu zuba jari.
  • Ci gaba da samar da ruwan sha musamman a yankunan karkara.