1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Adeyemo ya ce Amurka ta kakaba sabbin takunkumai kan Rasha

Mouhamadou Awal Balarabe
August 23, 2024

Wasu daidaikun 'yan Rasha da kanfanoni da ke kula da fasahar tsaro na cikin jerin wadanda takunkuman na Amurka suka shafa, don rage kaifin tallafa wa matakin Moscow na yaki a Ukraine.

Karamin sakataren kudin Amurka Adewale Wally Adeyemo
Karamin sakataren kudin Amurka Adewale Wally AdeyemoHoto: Leah Millis/REUTERS

Cikin wata sanarda da ya fitar a Washington, mataimakin sakataren kudi na Amurka Wally Adeyemo ya ce takunkumin, wani yunkuri ne na tabbatar da alkawurran da shugaba Joe Biden da takwarorinsa na G7 suka yi na kawo cikas ga yunkurin Rasha na samar wa kanta da makaman da take yakan Ukarine da su. Wannan takunkumin karya tattalin arzikin ya shafi kamfanonin fasaha da wadanda ke hada-hadar kudi na Rasha.

Ma‘aikatar harkokin wajen Amurka na da niyyar mayar da hankali kan kamfanonin kasar Sin 15 da ake zargi da ci gaba da samar da kayayyakin ga masana'antun Rasha. Haka kuma ta sanar da rufe kofofin Amurka ga duk wadanda aka kakaba wa takunkumin.