AFCON: Zagayen dab da na karshe
January 12, 2026
Ba mu fara da wasannin Bundesliga da aka buga a karshen mako, inda Bayern Munich ta ci gaba da rike kambunta na saman tebur da maki 44 a mako na 16, bayan da ta karbi bakuncin Wolfsburg ta kuma caskara ta da ci takwas da daya. Yayin da Borussia Dortmund ke a matsayi na biyu a saman teburin na kakar Bundesliga ta bana da maki 33, bayan canjaras uku da uku a gidan takwararta Antracht Frankfurt. Duk da soke wasansu da aka yi ita da St. Pauli, har yanzu RB Lepzig na rike da matsayi na uku na teburin Bundesliga da maki 29.
Ita ma dai Borussia Mönchengladbach da ba ta fara kakar ta bana da kafar dama ba, ta yi nasara a gida da ci hudu da nema a wasanta da FC Augsburg. An tashi wasa Freiburg na da ci biyu Hamburg da ta yi tattaki zuwa gidanta na da ci daya, yayin da Stuttgart ta bi Bayer Leverkusen har gida ta kuma caskara ta da ci hudu da daya. Heidenheim ta karbi bakuncin FC Cologne a wasan da suka tashi canjaras biyu da biyu, haka abin yake a gidan Union Berlin da ta karbi bakuncin Mainz, inda suma suka tashi canjaras biyu da biyu. Wanna ne ma wasan da Abdulkarim Muhammad Abdulkarim da Abdul-raheem Hassan suka kawo muku kai tsaye daga nan sashen Hausa na DW, ga kuma kadan daga yadda ya gudana.
A gasar Premier League ta Ingila kuwa, har yanzu kungiyar Arsenal ke ci gaba da rike kambunta na saman tebur da maki 49, yayin da Manchester City ke ci gaba da mara mata baya a matsayi na biyu da maki 43. Aston Villa ta rike matsayinta na uku da kyau, ita ma da maki 43. Sai dai a yayin da aka shiga mako na 21 na kakar ta Premier League za a iya cewa Liverpool da ba ta fara kakar ta bana da kafara dama ba ta farfado, inda a yanzu ta hawo saman tebur a matsayi na hudu da maki 35.
A LaLiga ta kasar Spaniya kuwa, Real Madrid ta kwashi kashinta a gidan Bercelona a wasan da suka fafata a yammacin Lahadi da ci uku da biyu. Wannan nasara da Bercelona ta yi, ta sanya ta ci gaba da zama daram a saman teburin LaLiga da maki 49, yayin da 'yan gidan madarar wato Real Madrid ke take mata baya a matsayi na biyu da maki 45. Villarreal CF da ta karbi bakuncin Deportivo Alaves ta kuma caskara ta da ci uku da daya ce ke a matsayi na uku da maki 41.
Idan muka koma nahiyar Afirka kuwa, Maroko mai masaukin baki da Najeriya da Masar da kuma Senegal ne, za su fafata a wasan kusa da na karshe a gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Nahiyar Afirka AFCON. Wakilinmu na Bauchi a Tarayyar Najeriya, Aliyu Muhammad Waziri ya yi mana nazari kan yadda wasan kusa da na kusa da na karshe wato Quater Finals ya gudana da ma yadda za a fafata wasan na Semi Final a ranar Larabar da ke tafe.
Daga ranar Lahadi mai zuwa 18 ga wannan wata na Janairu ake fara gasar neman cin kofin Tennis na Australían Open har zuwa ranar daya ga watan gobe na Febrairu. Wannan gasa ta Australian Open na daya daga cikin manyan wasannin tennis da suke gudana duk shekara, kuma na Australiya ake farawa a birnin Melbourne na jihar Victoria da ke kasar ta Australiya. Duk wanda ya samu nasara zai samu makudan kudi kimanin dala milyan hudu da 150,000 wanda yake matsayi na biyu kuma dala milyan biyu da 150,000 sannan duk 'yan wasu za su samu karin kimanin kaso 10 cikin 100, idan aka kwatanta kudin da suka samu a shekarar da ta gabata.
An zabi Max Verstappen a matsayin zakaren matukin motocin tseren Formula One na duniya na shkearar da ta gabata, sakamakon kuri'ar da 'yan uwansa matuka motoci suka kada, inda haka ke zama karo na biyar a jere ke nan da Verstappen ya samun wannan matsayi mai daraja tsakanin shahararrun mutuka motocin tsere na duniya. Sannan Lando Norris na tawogar McLaren ya samu matsayi na biyu, sauran da suka ciki manyan matsayi zuwana biyar akwai George Russell, da Oscar Piastri, da kuma Charles Leclerc.
Rahotanni daga Italiya na nuni da cewa, wani mai gadi a wajen da ake aikin shirye-shiryen gudanar da gasar Wasannin Guje-guje da Tsalle-tsalle na Lokacin Hunturu na wannan shekara ta 2026 ya rasa ransa. Ministan kula da kayan more rayuwa na kasar Matteo Salvini da ya tababbar da afkuwar lamarin da ya faru a tsibirin shakatawa na Cortina d'Ampezzo, ya bukaci da a gudanar da cikakken bincike kan rasuwar mai gadin mai shekaru 55 a duniya da ya rasu cikin dare a yayin da yake bakin aikinsa. An bayyana cewa, hasashen masana yanayi ya nuna cewa a daren da mai gadin ya rasu, yanayi na kasa da digo 12 a ma'aunin Celsius a yankin.