1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Siyasar Jamus: AfD na zawarcin matasa

September 20, 2024

Yayin da al'ummar jihar Brandenburg da ke gabasahin Jamus ke shirin tunkarar zaben jihar, jam'iyyar AfD mai tsananin kishin kasa da kyamar baki ta kuduri aniya tare da fatan samun karbuwa musamman a tsakanin matasa.

Jamus | Zabe | Brandenburg | AfD
Jam'iyyar AfD mai kyamar baki, na samun karbuwa a JamusHoto: Daniel Lakomski/IMAGO

Alamomin jam'iyyu da tambari iri-iri da ke alamta yanayin kankamar harkokin siyasa, sun cika birnin Brandenburg. Jiha ta biyar mafi girma a Jamus, kuma ta 10 a yawan mutane da yawansu ya kai miliyan biyu da dubu 500. Alamu sun nuna cewa matasa ka iya yin tururuwa wajen dangwala wa jam'iyyar AfD kuri'a a ranar zaben, lamarin da ke zama tarnaki ga samun nasarar jam'iyyar SDP. Tuni ma dai wani matashin 'dan takara a jam'iyyar mai shekaru 24, Kurt Fischer ke nuna fargabarsa a kai. A kokarinsa na janyo hankalin matasan mazabarsa zuwa jam'iyyarsa ta SDP, Fischer ya dauki gabaren aike wa masu yin zabe a karon farko wasikar gayyatar zuwa shagalin gashin nama don rakashewa. Ya shaida cewa batun yakin neman zabe da yada angizo ta Internet, wani lamari ne mai tarin kalubale ga jam'iyyun.

Matashi Kurt Fischer dan takara a jam'iyyar SPD mai mulki a JamusHoto: Fionn Große

Jam'iyyar AfD ta yi nisa wajen yada faya-fayan bidiyo a shafukan sada zumunta, ta hanyar amfani da kirkirarriyar fasahar AI da ke haska irin barazanar da Jamusawa fararen fata ke fuskanta daga bakin haure. Batun kenan da Mr Fischer ke matukar adawa da shi, inda kuma kididdiga ta nunar da cewa ko wane daya daga cikin matasa uku zai kadawa AfD kuri'a a zaben da ke tafe. 'Ya'yan jam'iyyar sun dukufa wajen yaki da kalmomin da ake jifan AfD din da su, wadanda suka shafi wariyar launin fata. Kwanaki kalilan dai su ka rage a gudanar da wannan zabe, wanda kuma har zuwa wannan lokaci akwai tarin matasan da ba su kai ga yanke shawarar wacce jam'iyya za su zaba ba lokaci ne kawai zai tabbatar da ko me zai faru.