AfD na son karfafa Addinin Kirista a Jamus
May 29, 2025
Ita dai jam'iyyar AfD ta Jamus galibi tana nuna yadda aka samu 'yan gudun hijira Musulmi daga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya tun daga shekara ta 2015, wadanda suka tumbatsa kuma al'adunsu na adinin Islama ke karo da al'adun Jamusawa da ke da alaka da adinin Kirista kuma irin wannan matsala gabili ake fuskanta a sauran kasashen Yammacin Duniya.
Wannan yanayi ya janyo musu matsanacin ra'ayi samun kwarji a siyasance, kuma suna ci gaba da amfani da wannan dama. Matthias Kortmann masanin zamantakewar dan Adam a Jami'ar Dormund da ke Jamus, ya bayyana abin da yake karfafa matsayin masu matsanancin ra'ayin.
A watan Janairun wannan shekara ta 2025 jam'iyyar AfD ta gudanar da taro a jihar Saxony, inda jaridun Jamus suka nuna yadda jam'iyyar ta kara zama mai matsanancin ra'ayi. A wajen taron shugabar jam'iyyar Alice Weidel ta nuna muhimmancin koyar da Addinin Kirista da yadda haka yake ci gaba da taka rawa mai tasiri a rayuwarta kuma tana ci gaba da zurfafa bincike game da addini.
Ita dai jam'iyyar AfD tana kara cusa tsoro, musamman sakamakon karuwar yawan Musulmi da suka shiga kasar ta Jamus da al'adunsu da suka saba da na Jamus. Ita dai kasar Jamus tana da mutane kimanin milyan 83, kuma alkaluman hukuma na shekara ta 2020 ya nuna daga ciki akwai mabiya Addinin Islama kimanin milyan biyar da rabi.